• Mon. Jul 4th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

PDP TA CACCAKI MINISTAN SUFURIN NAJERIYA BISA KALAMAN CIN HANCI

Babbar jam’iyyar adawar Najeriya PDP ta caccaki ministan sufuri Rotimi Amaechi kan kalaman da ya yi cewa irin cin hanci da Rashawa da a ka tabka a karkashin PDP ya fi wanda ke gudana a karkashin gwamnatin APC mai ci.

PDP ta sanarwar kakakin ta Kola Ologbondiyan ta ce hakan na nuna a na cin hanci da rashawa a boye a gwamnatin ta APC.

Amaechi a zantawar ya nuna kamar ya na daga nasarar shugaba Buhari yanda masu rashawa ba sa iya fitowa su baje kolin su satar su a gaban jama’a.

PDP ta yi amfani da damar don cimma muradun siyasa inda ta ce ai gara PDP da kan baiyana almundahana da APC da ke yin badakala cikin sirri.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “PDP TA CACCAKI MINISTAN SUFURIN NAJERIYA BISA KALAMAN CIN HANCI”

Leave a Reply

Your email address will not be published.