Jam’iyyar PDP mai adawa ta shigar da kara babbar kotun taraiya a Abuja ta na bukatar soke jam’iyyar APC don zargin cewa ta saba ka’idar tsarin shugabanci.
PDP na cewa APC na da mutum 13 ne da ke jagorantar ta a kwamitin gwamna Buni wanda ya dace a ce mutum 24 ne a cikin kwamitin.
PDP ta na bukatar babbar kotu ta soke rejistar ta PDP da nuna duk aiyukan da kwamitin riko ya yi bai tafi bisa tsarin doka ba.
Zuwa rubuta labarin nan, ba a mika karar ga wani alkali ba.
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀