• Sun. Nov 28th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

PDP-OYINLOLA KA IYA GADON SECONDUS

ByHassan Goma

Sep 12, 2021 , , ,

Tsohon gwamnan Osun Olagunsoye Oyinlola ka iya gadon jinginennen shugaban babbar jam’iyyar adawa ta PDP Uche Secondus.

Sunan Oyinlola ya fito ne a taron majalisar kolin jam’iyyar inda duk sassa su ka ajiye muradun su don mara baya ga tsohon gwamnan.

Oyinlola wamda ya zama gwamnan Osun a 2003 ya kuma zarce a 2007 har kotu ta sauke shi a 2010 ta dora Rauf Aregbesola, ya cika shekaru 70 a watan Febreru.

Wannan ya nuna Oyinlola zai iya zama sabon shugaban PDP a babban taron da za ta gudanar a watan gobe.

Kazalika hakan na nuna har yanzu PDP za ta iya barin tikitin takarar shugaban kasa a yankin arewa a 2023.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *