• Mon. Jul 4th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

PANTAMI YA TAIMAKAWA SHUGABAN EFCC A LOKACIN DA YA CARKE A YAYIN JAWABI A ASO ROCK

 

Mnistan sadarwa da tattalin arzikin zamani Isa Pantami ya taimakwa shugaban hukumar yaki da cin hanci EFCC Abdulrashid Bawa a lokacin da ya carke kan mumbarin jawabi a taron shaidar dan kasa da a ka gudanar a fadar Aso Rock.

Farfesa Pantami ya yi wuf ya rako Bawa da dawo shi kan kujerar sa ya zauna don farfadowa daga halin da ya shiga na shidewa mai tada hankali.

Abdulrashid Bawa dai na cikin bayani kan wani mutum da su ka kama a kudancin Najeriya dauko da katunan layin waya wajen 160; daga nan sai ya dafa kirji da kuma kan sa kamar ya samu bugun zuciya.

Da Bawa ya kasa cigaba da jawabin, ya ce a nan zai dakata don ba zai iya cigaba da magana ba inda ya yunkura da taimakon mutane ya koma kujerar sa.

Rahotanni sun baiyana cewa an garzaya da shi asibiti don gano ainihin abun da ke damun sa.

Kakakin EFCC Wilson Uwujeren ya ce Bawa na nan lafiya kalau.

Daga bisani Bawa ya shaidawa manema labaru daga gidan sa cewa ya hajijiya ce y ji lokacin jawabin shi ya sa ya dakata kuma likitoci sun tabbatar ma sa komai ya daidaita sai dai ya yi ta kwankwadar ruwa.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
2 thoughts on “PANTAMI YA TAIMAKAWA SHUGABAN EFCC A LOKACIN DA YA CARKE A YAYIN JAWABI A ASO ROCK”

Leave a Reply

Your email address will not be published.