• Sun. Dec 5th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

PALASDINAWA SUN BUKACI SAKO DAN UWAN SU DA ISRAILA TA KAMA KUMA YA KE YAJIN CIN ABINCI

ByNoblen

Nov 11, 2021

Bayan shafe kwana 112 Bapalasdine Miqdad Al-Qawasmi ya na daure a hannun hukumomin Isra’ila, Palasdinawa sun bukaci a sako shi da sauran masu yajin cin abinci.
Al-Qawasmi ya rame har ya koma rabin yanda ya ke don ruwa da gishiri kawai ya ke sha a tsawon lokacin.
Masu yajin cin abincin na nuna rashin amincewa da wani tsari na yanda Israila kan kama Palasdinawa ta rike su har tsawon kwana 60 ba tare da zuwa kotu ba kuma ta kan iya sabunta kwanakin.
Majalisar dinkin duniya da kungiyar taraiyar turai sun soki tsarin da nuna babu adalci.
An kama Al-Qawasmi ne don samun sa da hulda da kungiyar gwagwarmayar Palasdinawa ta Hamas.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *