• Mon. Jul 4th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

PALASDINAWA-ELSISI DA BENNET SUN YI TARO A SHARM  EL-SHEIKH

A wani yanayi mai nuna za a farfado da tattaunawa ta samar da fahimtar juna tsakanin Palasdinawa da Yahudawa, shugaban Masar Abdel Fatah Alsisi ya gana da firaministan Israila Naftali Bennet a yankin nan na shakatawa na Sharm El-Sheikh a Masar din.

Wannan shi ne karo na farko a shekaru 10 da wani jagoran Israila ke shigowa Masar da ke makwabtaka da yankin Palasdinawa.

Elsisi a ganawar ya jaddada tsohuwar hanyar neman kafa kasar Palasdinawa da ta Israila; a matsayin mafita ga yanda Israila ke mamaye yankunan Palasdinawa da hakan ke kawo zubar da jinin akasari daga yankin Palasdinawa.

A baya- bayan nan Israila ta tada jirage 160 su ka yi ta luguden wuta kan yankin Gaza da sunan neman tsagera da ke ma ta barazana.

Duk da faduwar tsohon firaministan Israila Benjamin Netanyahu ya kawo fatar sulhu, amma masu sharhi duk shugabannin Israila na da muradin mamaya iri daya.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “PALASDINAWA-ELSISI DA BENNET SUN YI TARO A SHARM  EL-SHEIKH”
  1. I have learn a few excellent stuff here. Definitely price bookmarking for revisiting.
    I surprise how much attempt you put to create any such fantastic
    informative site.

Leave a Reply

Your email address will not be published.