• Thu. Dec 9th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

PAKISTAN TA DATSE MANYAN TITUNA A BABBAN BIRNIN KASAR ISLAMABAD DON HANA ZANGA-ZANGAR KUNGIYAR TLP

ByNoblen

Oct 23, 2021

Hukumomi a Pakistan sun dau matakin datse manyan tituna a babban birnin kasar Islamabad don dakile fantsamar masu zanga-zanga na wata kungiyar gwagwarmayar Islama mai suna Tehreek-e-Labbaik Pakistan.
Masu zanga-zangar kungiyar ta TLP a takaice sun a bukatar a sako shugaban su ne Saad Rizvi da gwamnati ta kama da kuma korar jakadan Faransa a kasar don yada zanen batanci ga Manzon Allah mai tsira da aminci da mujallar Charlie Hebzo ta yada bara.
Masu zanga-zangar sun taso daga Lahore da ke yankin Punjab inda kungiyar ke da tagomashi.
Tun kama Saad Rizvi a watan yuni, zanga-zanga ta barke a kasar inda ‘yan sanda 6 su ka rasa ran su yayin da mutum 800 su ka samu raunuka.
Kakakin TLP Saddam Bukhari ya ce sun taso da dubban mutane daga Lahore sun nufi birnin Islamabad don aiyana matsayar su.
Jami’an tsaro sun tare mashigun Islamabad da birnin Rawalpindi don hana masu zanga-zangar shigowa.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *