• Fri. May 20th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

OSINBAJO ZAI ZAMA MUKADDASHI A YAYIN DA NA KE LONDON DON GANIN LIKITA-SHUGABA BUHARI

Shugaban Najeriya ya baiyana cewa mataimakin sa Yemi Osinbajo zai zama mukaddashin sa a yayin da ya fice zuwa London don neman magani
Shugaban wanda tun farko ya kai ziyarar aiki Kenya kuma ya so ya wuce London kai tsaye daga Nairobi, ya dawo Abuja, inda daga nan ya dau haramar tafiya London.
Shugaba Buhari ya ce ba abun da zai tsaya a yayin da ba ya nan, don mataimakin na sa da taimakon sakataren gwamnati Boss Mustapha da shugaban ma’aikata na fadar sa Ibrahim Gambari za su kula da kasar.
Shugaban da kan je London a duk lokacin da ya ke bukatar ganin likita, zai zauna a can kimain mako biyu kafin dawowa gida.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.