• Sat. May 21st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

OSINBAJO YA MUSANTA MALLAKAR FILIN DA A KA GINA GININ DA YA RUGUJE

ByYusuf Yau

Nov 8, 2021

Mataimakin shugaban Najeriya Yemi Osinbajo ya musanta mallaka ko wata alaka da filin da a ka gina ginin nan mai hawa 21 da ya ruguje a anguwar Ikoyi a Lagos.

Rugujewar ginin ta yi sanadiyyar mutuwar fiye da mutum 30 inda wasu kuma su ka samu raunuka.

Jaridar Sahara ta ruwaito labarin mallakar filin ga mataimakin shugaban kazalika mai kwangilar ginin ma Femi Osibona ma dan barandar Osinbajo ne.

Kakakin mataimakin shugaban Laolu Akande ya ce sharri ne a ka kullawa mataimakin shugaban don duk abun da ya mallaka an baiyana.

Wannan dai ya sa mataimakin shugaban ya ce ya sanar da lauyoyin sa don daukar mataki kan jaridar sahara.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.