• Mon. Jan 17th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

OLUBADAN YA RIGA MU GIDAN GASKIYA

ByNoblen

Jan 3, 2022 ,

Babban basaraken masarautar Ibadan a jihar Oyo Saliu Adetunji ya riga mu gidan gaskiya a asibitin koyarwa na jami’ar Ibadan bayan fama da jinya.
Marigayin ya zama sarkin Ibadan na 41 a shekara ta 2016.
An haifi marigayin ne a 1928 kuma shi ne babba a cikin ‘ya’yan mahaifin sa 17.
Wani abun tarihi ga Olubadan Adetunji shi ne tela ne da ke yawo kan titunan Lagos ya na dinke ‘yan kayayyaki kuma bai yi karatun zamani ba, amma Allah ya hukunta ya jagoranci daya daga manyan masarautun Yarbawa.
Duk da Adetunji na kaunar manufofin Yarbawa amma ya yaki neman kasar Yarbawa ta Odudua ta halin tada fitina.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *