• Fri. Oct 7th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

OHANEZE NDIGBO TA GANA DA SHUGABA BUHARI A EBONYI

Shugabannin kungiyar kare muradun Igbo Ohaneze Ndigbo sun gana da shugaba Buhari a Abakaliki babban birnin jihar Ebonyi.
Shugaban kungiyar George Obiozor ne ya jagoranci jama’ar sa zuwa wannan tattaunawa da hakika ta shafi batun neman sako shugaban ‘yan awaren Biyafara Nnamdi Kanu da ke hannun jami’an tsaron DSS kuma ya ke fuskantar shari’ar cin amanar kasa.
Kazalika batun shugaba Buhari ya taimaka mulkin Naeriya ya koma kasar Igbo a 2023.
Shugaba Buhari dai na ba da tabbacin mika ragama ne ga wadanda ‘yan Najeriya su ka zaba kuma kan Kanu ya ce ba ya saka baki kan lamuran da ke hannun kotu.
Gwamnann jihar ta Ebonyi Dave Umahi da ke takarar shugaban kasa a APC na wajen taron.
Shugaba Buhari ya na jihar Ebonyi ne kan ziyarar aiki na tsawon wuni biyu inda hakan zai sa ya gana da shugabannin Igbo a yankin su.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “OHANEZE NDIGBO TA GANA DA SHUGABA BUHARI A EBONYI”

Leave a Reply

Your email address will not be published.