• Wed. Jun 29th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

NNPC TA CE BA KARIN FARASHIN LITAR FETUR A WATAN GOBE

Kamfanin fetur na Najeriya NNPC ya ce babu batun kara farashin litar fetur a watan gobe na Mayu.

Shugaban kamfanin Mele Kyari Kolo ya baiyana don kokarin kwaranye zullumin jama’a na yiwuwar karin farashin da mafi tsada a tarihi.

Kamar batun kwaranye fargabar na zuwa ne wata-wata kamar yanda Kolo ya ce ba kari a watan nan na Afrilu.

Duk wannan ba zai yaye dukkan damuwa ba, tun da NNPC bai ce gaba daya ba ma batun karin ba.

Mele Kolo ya ce gwamnati na kashe biliyoyin Naira don farashin ya zauna yanda ya ke a yanzu lita Naira 162. 

Kolo ya nuna a karshe dai ba da tallafin ba zai dore ba.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.