• Fri. May 20th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

NNAMDI KANU YA KASA SAMUN SA’IDAR MAIDA SHI GIDAN YARI DAGA HANNUN DSS

ByNasiru Adamu El-hikaya

Oct 22, 2021

Babbar kotun taraiyar Najeriya Abuja ta ki amincewa da bukatar shugaban ‘yan awaren Biyafara Nnamdi Kanu na a tura shi gidan yarin Kuje daga hannun jami’an tsaron DSS da ya gaji da zama a hannun su.
Kanu ya mika bukatar yayin da a ka kawo shi babbar kotun taraiya don sauraron shari’ar da a ke yi ma sa da yanzu ta hada da tuhumar cin amanar kasa da kuma ta’addanci.
Wadannan laifukan biyu na da hukunci mafi tsanani in an samu mai yi da laifin da a cajin sa da shi.
Kotun ta ajiye ranar 10 ga watan gobe don sauraron sabon cajin da a ka hadawa Kanu.
Lauyoyi da ‘yan jarida ba su samu damar shiga kotun ba don yanda jami’an tsaro su ka dau tsauraran matakan hana hakan.
Wani rahoto ya nuna a wajen kotun wasu matasa sun nemi lallasa mawallafin jaridar sahara Omoyele Sowere wanda ke zanga-zangar juyin juya hali da jami’an tsaro ke daukar hakan a matsayin yunkurin kifar da gwamnati.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.