• Mon. Jul 4th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

NEMAN TANTANCE ADAMS A MATSAYIN KWAMISHINAN ZABE YA TADA YAMUTSI

Yunkurin tantance Farfesa Sani Adams a matsayin kwamishinan zabe daga kwamitin majalisar dattawa ya tada yamutsi.

Jaridar PUNCH ta ruwaito cewa shugaban kwamitin Sanata Kabiru Gaya ya so ya tantance Adams amma hakan bai samu karbuwa ba a majalisar.

In za a tuna kwamitin majalisar tun farko ya jingine tantance Sani Adams da Lauretta Onochie saboda matsaloli da a ka samu na cikas ko saba ka’ida ga tantancewar.

Yayin da Lauretta Onochie ta kasa tsallakewa don akwai kwamishinan hukumar zabe a yanzu haka daga jihar ta; Sani Adams na fuskantar tuhumar cin zarafi yayin da ya ke koyarwa a jami’ar Jos.
Tuhumar Adams na gaban kotun koli.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
2,579 thoughts on “NEMAN TANTANCE ADAMS A MATSAYIN KWAMISHINAN ZABE YA TADA YAMUTSI”