• Sat. May 21st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

NEMAN RABA KASA BA DABARA BA CE DON KANANAN KASASHE MA NA NEMAN HADEWA DA MANYA NE-OSINBAJO

 

Mataimakin shugaban Najeriya Yemi Osinbajo ya ce raba kasa a yanzu ba dabara ba ce don kananan kasashe na neman hadewa da manya ne.

Osinbajo na magana ne a ofishin jakadancin Najeriya da ke Burtaniya ga wasu jami’an Najeriya.

Yemi Osinbajo ya ce yanda Najeriya ke da albarkatun kasa, ba daidai ba ne wani ya na tunanin raba kasar a matsayin wani abu mai alheri.

Don haka Osinbajo ya ce yarbawa ba za su yi rayuwa su kadai ba, hakanan Igbo ko mutan arewa don kowa na bukatar dan uwan sa.

Mataimakin shugaban kasa ya yi takatsantsan wajen zaiyana cewa ba mamaki shugaba Buhari ne mafi farin jini a tarihin siyasar Najeriya.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.