• Mon. May 23rd, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

NDLEA DA MA’AIKATAR SHARI’A DUK NA DA KARA KAN ABBA KYARI

Zuwa litinin din nan mai zuwa hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta Najeriya NDLEA za ta shiga kotu don shari’ar DCP Abba Kyari.
Hukumar wacce ta ke rike da Kyari tun 12 ga watan jiya, na son kotu ta tabbarwa Kyarin laifin cinikin miyagun kwayoyi bayan nuna wani faifan bidiyo da ta yi da ke nuna DCP Kyari na magana kan hodar iblis mai nauyin kilogiram 25.
Wannan na zuwa ne bayan ministan shari’a Abubakar Malami ya gabatar da karar bukatar hukuncin kotu na mika Kyari ga Amurka don fuskantar tuhumar mu’amala da damfara.
Jami’an NDLEA na nuna batun mika Kyari ga Amurka ba zai dakatar da shari’ar da su ke son a yi wa Kyari ba don nun aba tababa kan zargin da su ke yi wa shaharerren dan sandan.
Kokarin da mu ka yi na ganin Kyari ko sanin ainihin inda a ke tsare da shi bai yiwu ba don jami’an NDLEA na daukar duk matakan gudanar da aikin su ba da samun cikas ba.
Kyari dai bai yarda da duk tuhumar da a ke yi ma sa ba, inda ya nemi beli, amma bai samu nasarar samun belin ba.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “NDLEA DA MA’AIKATAR SHARI’A DUK NA DA KARA KAN ABBA KYARI”

Leave a Reply

Your email address will not be published.