• Thu. May 19th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

NAJERIYA TA KUSA KAMMALA RIGAKAFIN KORONA GA RUKUNIN GWAJI

A yanzu haka Najeriya na dab da kammala rigakafin korona ga rukunin farko na gwaji da ya fara daga kan manyan jami’an gwamnati da ‘yan kwamitin yaki da cutar na taraiya.

Alkaluman hukumar lafiya matakin farko na nuna an yi allurar ta zagayen farko ga mutum miliyan 1,945,273 da ya zama kashi 96.7%.

Hakanan an suma yi wa mutum dubu 22, 162 rigakafin zagaye na biyu kuma na karshe da ke nuna kammala rigakafin ga mutumin da ya samu sau biyu.

Akalla wadanda a ka yi wa rigakafin na ji a ran su sun samu ka riya daga cutar ta annoba.

Mutane da dama na nuna kin jinin rigakafin don fargabar gudun samun rama a neman kiba da ya sa su kaucewa duk hanyar da za su samu allurar.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.