• Mon. Jul 4th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

NAJERIYA NA SHIRIN SAMUN KARIN ALLURAN RIGAKAFIN KORONA

Gwamnatin Najeriya ta baiyana cewa ta na shirin karbae karin alluran rigakafin korona bairos daga shirin nan na samawa kasashe masu tasowa allurar mai taken COVAX.

Shugaban hukumar lafiya matakin farko ta Najeriya Dr.Faisal Shu’aib ya baiyana cewa Najeriya na sa ran samun allurai miliyan 3.92 na AstaraZeneca da ta ke amfani da shi.

Dr.Shu’aib ya ce alluran za su iso zuwa farkon watan agusta mai zuwa.

Dama Najeriya ta samu alluran miliyan hudu inda ta ke gaba da kammala yin zagaye na biyu na rigakafin ga mutum miliyan 2.

Rigakafin ya shafi manyan jami’an gwamnati da ma’aikatan lamuran lafiya da wasu fitattaun mutane da ke harkokin yau da kullum da su ka shafi jama’a.

Har yanzu akwai miliyoyin mutane da ke dari-dari da karbar rigakafin don tunanin kar garin neman kiba a samo rama.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “NAJERIYA NA SHIRIN SAMUN KARIN ALLURAN RIGAKAFIN KORONA”

Leave a Reply

Your email address will not be published.