• Fri. Dec 2nd, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari...

NAJERIYA NA DAUKAR MATAKAN MIKA DCP ABBA KYARI GA AMURKA

Gwamnatin Najeriya na daukar matakan mika shaharerren dan sanda DCP Abba Kyari ga kasar Amurka don fuskantar tuhumar hada kai da dan damfara Ramon Abbas wanda a ka fi sani da Hushpuppi.
Ministan shari’a na Najeriya Abubkar Malami ya shigar da bukatar mika Kyari ga Amurka gaban babbar kotun taraiya don yanke hukuncin alkali.
Tun farko hukumar binciken manyan laifuka ta Amurka FBI ta tura shaidar hannun Kyari a damfarar Hushpuppi da neman Najeriya ta mika shi don a yi ma sa shari’a a Amurka.
A yanzu haka Kyari na hannun hukumar yaki da fataucin miyagun kwayoyi don tuhumar mu’amala da fataucin hodar iblis da nauyin ta ya kai kilogiram 25.
Kyari wanda ya yi matukar suna a lamuran kama ‘yan damfara da fito na fito da barayi, ya kalubalanci tuhumar da a ke yi ma sa da nuna sharri ne kawai don hassada.
Lauyoyin Kyari sun bukaci a ba da belin sa don kare hakkokin sa na dan-adam, hakanan da nuna godewa irin sadaukar da ran sa da ya yi a matsayin dan sanda ga lamuran tsaron kasa.
Irin shari’ar nan ta neman mika wani ketare na iya tafiya har kotun koli.

KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *