• Fri. Dec 2nd, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari...

NAJERIYA NA DA NIYYAR KWASO JAMA’AR TA DAGA UKRAINE-GARBA SHEHU

Mai taimakawa shugaban Najeriya kan labaru Garba Shehu ya ba da tabbacin gwamnati na daukar matakan ganin an dawo da ‘yan Najeriya da su ka makale a kasar Ukraine da ke fuskantar mamaya daga kasar Rasha.
Shehu ya ruwaito ministan wajen Najeriya Goerfrey Enyeama na ambata daukar mataki don dawo da ‘yan Najeriya da ke Ukraine musamman dalibai.
Tun farko ministan ya bukaci ‘yan Najeriya su kwantar da hankali don hare-haren Rasha na shafar sassan cibiyoyin tsaro ne.
Dalibai na nuna fargaba yakin ka iya kawo mu su barazana don haka su ke bukatar ma’aikatan wajen ta dawo da su gida.
Majalisar wakilai ma ta yi kira ga gwamnatin ta gaggauta jigilar daliban zuwa gida don sun bugo waya su na masu baiyana bukatar kawo mu su dauki.

KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *