• Sat. Jul 2nd, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

NAJERIYA BA TA DA ZARATAN SOJOJI-MANJO ALMUSTAPHA

Tsohon babban mai kare lafiyar marigayi shugaban mulkin soja na Najeriya Janar Abacha wato Manjo Hamza Almustapha ya ce Najeriya ba ta da zaratan sojoji don yanda a ka yi sakaci kan hakan tsawon shekaru.
Manjo Almustapha wanda ya ke magana a yayin aiyana takarar shugabancin kasa a jam’iyyar AA, ya ce barin sojoji da ‘yan sanda a baya su ka yi aikin hadin guiwa na fiye da shekara daya ya sa sojojin sun kwalance da daukar dabi’u irin na ‘yan sanda.
Almustapha ya kara da cewa su kuma ‘yan sanda sun sauya daga aiyukan kare fararen hula sun sau wasu dabi’u na soja da hakan ya saka su ka sauka daga tsarin aikin su na hulda da farar hula.
Don haka Almustapha ya bukaci ya bukaci yin garambawul a lamarin sojoji da ‘yan sanda don samun tsaro yanda ya dace.
Shaharerren sojan ya nuna fargabar mallakar ma’adinai musamman zinari ya sa wasu kasashe ke yi wa yankin arewacin Najeriya makarkashiya.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
3 thoughts on “NAJERIYA BA TA DA ZARATAN SOJOJI-MANJO ALMUSTAPHA”
  1. Thank you for any other fantastic article. The place else may just anyone get that type of info in such a perfect approach of writing? I’ve a presentation subsequent week, and I’m on the search for such information.

  2. Hello, Neat post. There is a problem with your web site in web explorer, would test this?K IE nonetheless is the market chief and a large section of other people will miss your great writing because of this problem.

Leave a Reply

Your email address will not be published.