• Sun. Jan 16th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

NAIRA TA SULMUYO KASA A KASUWAR CANJI KAN DALAR AMURKA

ByNoblen

Dec 14, 2021 ,

Bayan samun tsawon mako Naira na tsaya a farashi daya wato Naira 565 kan dalar Amurka yanzu ta samu koma baya na bazata.
A binciken farashi a kasuwar canji a Lagos a farkon makwan nan na nuna yanzu dala daya na tashi kan Naira 572.
Wannan na neman dusashe hasashe ko fatar wasu masu sharhi cewa dalar zuwa karshen shekarar nan za ta fado tun da a watan jiya ta sauko zuwa Naira 540 har ma kasa da hakan wato wajen 530.
In ka debe Karin farashin man fetur, baa bun da kan zama dalilin tashin farashin kayan masarufi a Najeriya irin tashin farashin dala kan Naira.
In za a tuna babban bankin Najeriya ya daina ba da dala ga kasuwar canji inda ya bukaci duk mai son dala ya nufi bankin sa don samun ta kan farashin hukuma.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “NAIRA TA SULMUYO KASA A KASUWAR CANJI KAN DALAR AMURKA”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *