• Sat. May 21st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

NAIRA TA KARA SAMUN NAKASU DAGA MATAKIN BABBAN BANKIN NAJERIYA

Babban bankin Najeriya ya dau wani matakin kara rage darajar Naira da hakan zai sa dala ta kara tsada a canjin hukuma da na ‘yan kasuwa.

Dama a ‘yan watannin nan Naira ta kasa motsi inda dala ke nausawa gaba da sauran manyan kudin duniya irin Fam din Ingila da Euro na turai.

Rage darajar Naira ba ya rasa nasaba da bin ka’idojin tattalin arziki da lamuni na hukumar lamuni ta duniya IMF.

Rashin kera muhimman abubuwan da jama’a ke bukata a cikin gida; a sharhin masana tattalin arziki na daga manyan dalilan zubewar darajar Naira.

Yanzu haka a kasuwar canji dala daya kan tashi kan kimanin Naira 480.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.