• Mon. Jul 4th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

NAIRA TA CIGABA DA FADUWA KAN DALA

ByHassan Goma

Sep 17, 2021 ,

NAIRA TA CIGABA DA FADUWA KAN DALA

A tsawon lokaci Naira na cigaba da samun koma baya kan canjin dala inda zuwa yanzu a kasuwar canjin dala daya kan kai Naira 560-568.

Lamarin dai shi ne za a ce ya fi na kowane lokaci a baya muni don a wajajen shekara ta 2015 dala ta taba kai wa Naira 520 amma ta dauko ta dawo wajajen Naira 400 da ‘yan kai.

Akalla dai dala na wuyar samuwa a bankuna don wanda ya je fidda dala kan iya samun rabin abun da ya je nema musamman in dalar ta kai 2000.

Hakika wannan yanayi ya haddasa tashin farashin wasu muhimman kayan masarufi.

Babban bankin Najeriya dai dama ya dakatar da ba da dala ga kasuwar canji amma duk da haka kasuwar na cigaba da aiki daga wadanda ke ciro dalar daga ma’ajiyar su a banki ko a gida.

 

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
2 thoughts on “NAIRA TA CIGABA DA FADUWA KAN DALA”
  1. Hello There. I found your blog using msn. This
    is a really well written article. I’ll make sure to bookmark it and come back
    to read more of your useful information. Thanks for the post.
    I’ll certainly return.

  2. Hello there! Do you use Twitter? I’d like to follow you if that would
    be okay. I’m undoubtedly enjoying your blog and look forward to new posts.

Leave a Reply

Your email address will not be published.