• Thu. Dec 9th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

NAIRA BILIYAN 10.33: SAM BA KUDIN CETO NA ALBASHIN JIHAR KOGI EFCC TA MAYARWA CBN BA – GWAMNATIN KOGI

ByNasiru Adamu El-hikaya

Nov 22, 2021

Gwamnatin jihar Kogi ta ce sam kudin nan naira biliyan 19.33 da hukumar yaki da cin hanci EFCC ta gano kuma ta mayar da su babban banki ba na jihar ba ne.

EFCC dai ta ce ta gano kudin na biyan albashi ne na jihar Kogi da alamu su ka nuna ana neman salwantar da su ta maida su aljihun babban bankin Najeriya.
Kwamishina labarun jihar Kingsley Fanwo ya ce tun 2019 jihar ta raba kudin dauki na biyan albashin.
Kwamishinan ya ce jihar na bukatar EFCC ta janye matsayar ta cikin sa’a 48 ko jihar ta garzaya kotu.
Hakanan Fanwo ya ce EFCC ta na sane da cewa kudin ba su shafi jihar Kogi ba, don haka zargin na neman makirci ne da cimma muradun siyasa.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *