• Thu. Dec 9th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

NAFTALI BENNETT YA SHIGA OFISHIN FIRAMINISTAN ISRA’ILA YA FARA AIKI

Bayan tabbatar ma sa da nasara a majalisar dokoki, Naftali Bennett ya shiga ofishin firaministan Isra’ila ya fara aiki bayan kawar da dogon mulkin Benjamin Netanyahu.

Tsohon firaminista Netanyahu bai ji dadin kayen ba kuma bai yi wasu al’adun da a ka saba na raka firaminista ofis ba, inda har ma ya lashi takobin hambarar da sabwar gwamnatin nan ba ba dadewa ba.

Netanyahu na magana ne da ‘yan majalisar dokoki mafiya rinjaye na jam’iyyar sa ta Likud.

Yanzu dai koma me Netanyahu zai yi, ya bar mulki kuma dan takarar gamaiyar ‘yan adawa Bennett ya amshi ragama.

Madugun kulla yanda a ka yi waje rod da Netanyahu, wato Yair Lapid mai shekaru 57, yanzu shi ne ministan harkokin wajen Isra’ila.

Lapid zai amshi ragamar firaminista daga hannun Bennett mai shekaru 49 wanda dan addinin yahudawa ne na gargajiya a shekara ta 2023.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *