Shugaban kwamitin binciken dakataccen mukaddashin shugaban Hukumar yaki da cin hanci na Najeriya EFCC Ibrahim Magu, wato Jostis Ayo Salami ya yi watsi da labaran da wasu kafafe su ka yayata cewa ya yi nadamar karbar aikin binciken.
Ayo Salami a rubutaccen martanin da ya sanyawa hannu, ya ce bai taba wata hulda ko wakilta wani ya yi magana a madadin sa daga kwamitin binciken ba, don haka bayanin da a ka yayata na nadamar sa ba kamshin gaskiya a ciki.
A ‘yan kwanakin nan an yayata bayanin cewa Ayo Salami ya nuna nadama kan karbar aikin kwamitin binciken na Magu don kamar ya gano ba a yi wa Magu adalci ba.
Salami ya caccaki lauyoyin Magu da cewa su na cusa labarun karya a kafafen labaru don karkatar da hankalin jama’a kan zargin da a ke yi wa Magu na sabawa ka’idar aiki.
Jagoran kwamitin binciken, yace a matsayin san a tsohon shugaban kotun daukaka kara, ya jagoranci wasu shari’u da su ka fi wannan tsauri don haka ya dauki wannan aiki da ya ke yi da zuciya daya kuma da kasancewar hakan hidima ga kasa.
Jostis Salami ya bukaci ‘yan jarida su rika tantance labaru kafin yadawa bisa dokokin aikin su na adalci da tantance bayani.
Hakanan tsohon mai shari’ar ya yi alwashin cigaba da gudanar da binciken har sai an gano ainihin gaskiyar lamarin.