• Sat. May 21st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

NADA HAFSA YAHAYA: DA ALAMUN ZA A SAMU RITAYAR MANYAN JAMI’AN SOJA

Alamu na nuna nada Manjo Janar Farouk Yahaya a matsayin babban hafsan sojan kasan Najeriya zai kawo ritayar manyan hafsoshin soja da dama.

Wannan in ya faru ba zai zama abun mamaki don tsarin sojoji ba sa aiki a karkashin wanda su ka girma a aiki.

Manjo Janar Yahaya dan rukunin yaye sojoji na 37 inda a yanzu a na da sauran manyan hafsoshi a rukuni na 35 da 36.

Duk da haka ba lalle ne a yi wa manyan hafsoshin ritayar dole ba, za a iya ba su dama su zabi ajiye aiki da kan su ko a tura su wasu sassa da za su karisa aiki cikin lumana.

A ysnzu haka rahoto na nuna akwai wajen manyan hafsoshi 10 da ke gaba da sabon babban hafsan wadanda su ka hada da hafsan kula da sashen tsarin gudanarwa Manjo Janar Ben Ahanotu daga jiharvAnsmbra da hafsan sashen muliki Manjo Janar A.M Aliyu daga jihar Gombe.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.