• Mon. Jan 17th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

NA SAMU SAUKI DAGA CUTAR KORONA BAIROS-GARBA SHEHU

ByNoblen

Dec 31, 2021 ,

Mai taimakawa shugaban Najeriya kan labaru Garba Shehu ya fitar da sanarwar cewa ya samu sauki ko ya warke daga cutar korona bairos.
Shehu wanda a ka ba da labarin kamuwar sa da cutar da ma wasu mukarraban shugaba Buhari, ya baiyana godiya ga Allah da warakar da ya samu cikin gaggawa.
Garba Shehu ya godewa dukkan wadanda su ka yi ma sa addu’a ko nuna alhinin su ta kiran waya kan wannan cuta da ta same shi.
A nan Shehu, ya yi fatar duk ‘yan Najeriya da ke fama da cutar za su samu kwarin guiwar tsayin dakan yaki da cutar har su samu sauki.
In za a tuna a lokacin da Allah ya yi wa tsohon shugaban ma’aikata na fadar Aso Rock Abba Kyari rasuwa sanadiyyar korona, an hana wadanda su ka je jana’izar sa ciki har da Garba Shehu shiga fadar shugaban kasa na tsawon mako biyu don tabbatar da lafiyar su.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *