• Sat. Nov 27th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

NA JE GIDAN KALU NE DON ZANTAWA KAN NAJERIYA-TINUBU

ByYusuf Yau

Nov 22, 2021

Uban APC mai mulki a Najeriya Ahmed Tinubu ya baiyana dalilan da su ka sa ya ziyarci tsohon gwamnan Abia Orji Uzoh Kalu a Abuja.

Kalu dai da ke fuskantar tuhuma daga hukumar EFCC shi ne mai tsawatawa na majalisar dattawa.
Tinubu ya ce sun tattauna kan lamuran da kasa ke ciki da taimkawa matasa.
An yi ta yada labarin ziyarar da tunanin ta shafi burin Tinubu na yada muradun sa na son takarar shugabancin Najeriya a 2023.
Tinubu wanda ya dawo Najeriya daga jinyar da ta kai shi Burtaniya, ya shiga ziyarce-ziyarce har ma da zuwa fadar Aso Rock kan lamuran da a ke alakantawa da muradin takarar ta sa.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *