• Mon. May 23rd, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

NA FICE DAGA APC DON TA BAR TSARIN TA DA YA BAMBANTA DA PDP-DALUNG

Tsohon ministan matasa da wasanni na Najeriya Solomon Dalung ya ce ya fice daga jam’iyyar APC don barin tsarin da ta ke kai da ya saba da PDP.
Dalung wanda ya yi minista a wa’adi na farko na shugaba Buhari ya ce ya fice daga PDP ne a can baya ya shiga a ka kafa APC da shi don a kawo sauyi mai ma’ana.
Hakanan ya nuna APC ta koma hanyar PDP ba dauki dora da barin wasu kalilan su mamaye lamuran gwamnati.
Tsohon ministan ya kara da cewa ba lalle ne shugaba Buhari ne matsalar gwamnatin ba amma wadanda ya bari su ka zagaye shi da kan hana ruwa gudu.
An ga tsohon ministan a wajen taron masu son kafa jam’iyya ta uku mafi karfi a Najeriya.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “NA FICE DAGA APC DON TA BAR TSARIN TA DA YA BAMBANTA DA PDP-DALUNG”
  1. A person necessarily lend a hand to make seriously articles I might state. This is the first time I frequented your web page and thus far? I surprised with the research you made to make this particular publish extraordinary. Excellent process!

Leave a Reply

Your email address will not be published.