Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya nuna cewa ya damu kwarai da yanda lamuran tsaro ke tabarbarewa a sassan kasar nan.
Shugaban wanda ke magana bayan halartar sallar idin karamar sallah a barikin sojoji na Mambila, ya ce kalubalen na hana shi samun barci.
Shugaba Buhari ya nuna zai cigaba da dsaukar matakan da su ka dace don aminta kasar daga miyagun iri.
Hakanan shugaban ya yi magana a kan babban zaben 2023, ya na mai ba da tabbacin za a gudanar da zaben cikin adalci.
Shugaban ya halarci filin da wasu mukarraban sa inda babban limamin barikin Imam Muhammad Dahey Shuwa ya jagorantaci sallar da kira ga a dorewa da ayyukan kwarai da a ka gudanar a lokacin azumin watan ramadan.
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
Thankyou for this post, I am a big big fan of this site would like to proceed updated.