• Fri. May 20th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

NA BATA HANYAR GIDA NA DON YANDA A KA GYARA KADUNA-SHUGABA BUHARI

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce ya kasa gane hanyar zuwa gidan sa a Kaduna sanadiyyar gyara birnin da a ka yi.
Shugaban na magana ne a wajen kaddamar da aiyukan da gwamna Nasiru Elrufai ya aiwatar a tsawon shekaru 7 zuwa yanzu da ya hau mulkin jihar Kaduna.
Shugaba Buhari ya ce ya kauro Kaduna bayan kammala zaman gidan yarin sa a shekarun 1980 amma duk da tsawon lokaci ya kasa gano hanyar gidan sa don yanda gwamna Elrufai ya sauya fasalin garin.
Shugaban wanda ya kaddamar da sabuwar gadar Kawo da wasu aiyuka, ya shiga har Kafanchan inda ya kaddamar da aiyuka.
Kazalika a jumma’ar nan shugaban zai shiga Zaria inda zai kaddamar da wasu aiyuka kafin ya dawo Abuja.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “NA BATA HANYAR GIDA NA DON YANDA A KA GYARA KADUNA-SHUGABA BUHARI”
  1. Pretty section of content. I simply stumbled upon your web site and in accession capital to say that I
    get in fact loved account your blog posts. Any way I
    will be subscribing to your augment or even I success you get entry to
    constantly rapidly.

Leave a Reply

Your email address will not be published.