• Wed. Dec 1st, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

NA AMINCE DA ZAMA DAN AMSHIN SHATAN NAJERIYA-SHUGABAN NBC BALARABE SHEHU ILLELA

ByHassan Goma

Oct 6, 2021 ,

 

Shugaban hukumar kula da gidajen rediyo da talabijin na Najeriya NBC Mallam Balarabe Shehu Illela ya ce shi dan amshin shatan Najeriya ne ko al’ummar Najeriya.

Balarabe Illela na amsa tambaya ne kan zargin da wasu ke yi cewa hukumar ta NBC ‘yar amshin shatan muradun gwamnatin Najeriya ne.

Shugaban na NBC wanda ke ziyarar ganawa da kafafen labaru a ofishin Muryar Amurka na Abuja, ya ce im ba dokoki na hukumar ta NBC, wasu za su rika amfani da kafafen labaru don kawo tada fitina da rabuwar kawunan ‘yan kasa.

Illela ya dage da nuna cewa a Najeriya a na martaba kafafen labaru da ‘yan jarida, don in ba don haka da ‘yan jarida da daman a gidan yari.

Shugaban na NBC ya ce hukumar na yaki da labarun karya, cin zarafin jama’a da masu neman wargaza hadin kan kasa.

Hukumar wacce kwanan nan ta cika shekaru 29 da kafuwa ta yi wa kimanin kafafen labaru 700 rejista inda wajen 100 ke kan layi, yayin da a ka ki amincewa da bukatar lasisin wasu kafaofi 7.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *