• Fri. Jan 28th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

MUTUWAR SHUGABA IDRIS DERBY TA TADO JUYAYIN KISAN GILLA GA MO’AMMAR GHADDAFI

Rasa ran shugaban Chadi Idris Derby ta ta tado juyayin kisan gilla da a ka yi wa shugaban Libya Kanar Moammar Ghaddafi.

Duk da yanayin mutuwar shugabannin biyu na da bambanci, amma tsarin jagororin su da alakar su iri daya ce kuma su na da yanayi na jarumtaka da rashin jure sakarci sabanin wasu shugabannin Afurka.

Duk da gajiya da a ka yi da dogon mulkin Derby na fiye da shekaru 30, akalla a kan manta soja ne ko farar hula ne don yanda ya ke saka kaya da fita fagen daga da ‘yan ta’addan boko haram.

Ba a san ko mutan Chadi za su yi juyayin mutuwar Idris Derby a fagen daga da ‘yan tawaye ba, tun da tuni an nada dan sa Mahamat Kaka ya gaje kujerar sa.

Chadi har kullum na yanayi ne na fitina in an duba yanda tsohon shugaban kasar Hessen Hebre ya fice daga kasar ya ke zaman gidan yari a Dakar din kasar Senegal.

Har yanzu akwai gyauron shugabannin Afurka da su ka makale tsawon shekaru a kan mulki ba tare da jin duriyar su ba in ba an tashi batun ‘yan adawa ba kamar misalin shugaba Paul Biya na Kamaru.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *