• Thu. Dec 9th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

MUTUWA BABBAN WA’AZI NE GA JAMA’A-SHEIKH ABDULLAHI BALA LAU

Shaharerren malamin Islama a Najeriya Sheikh Abdullahi Bala Lau ya ce mutuwa babban wa’azi ne ga jama’a don hakika duk mai rai wataran zai gamu da mutuwa.

Imama Bala Lau wanda ya ke nasiha a makabartar Gudu Abuja bayan jana’izar kwamandan agaji  JIBWIS Lawal Sani, ya ce duk wadanda su ke kwance a makabartar za su so su tashi su yi nafila raka’a biyu su koma makwancin su.

Malamin ya ce don haka wannan ishara ce ga duk wadanda su ke raye su yi amfani da sauran damar su wajem dagewa ga ibada, gaskiya, rikwan amana da taimakawa juna.

Sheikh Bala Lau ya bukaci musulmi su rika raka marigaya zuwa makwancin su don hakan na da lada mai yawa.

Kafin ya fita daga makabartar, limamin ya ce kowa ya yi wa marigayin addu’a shi kadai don haka ne ya dace sa sunnah ba wani mutum daya ya na fada saura su na amasawa ba.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *