• Tue. Nov 30th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

MUTUM SHIDA DA A KA SACE A JAMI’AR ABUJA SUN KUBUTA

Jami’ar Abuja ta ba da labarin cewa mutum 6 da barayi su ka sace sun samu kubuta ba tare da biyan kudin fansa ba.

Mutanen sun hada da Farfesa Obansa Joseph da ‘ya’yan sa.

Jami’ar ta baiyana cewa an nemi kudin fansa Naira miliyan 300 kan mutanen, amma ba a biya ko sisin kobo ba a ka sako mutanen.

Babban dai labari an samu kubutar mutanen da biyan kudi ko ba biyan kudi.

Satar mutane na neman zama ruwan dare hatta a yankunan ba a tsammanin aukuwar irin wannan mugun aiki.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *