Rahoto daga jihar Delta na baiyana mutuwar mutum 4 a sanadiyyar wani abu da ya fashe ya hadddasa gobara a wata cibiyar iskar gas a jihar Delta.
Fashewar kazalika ta haddasa samun rauni ga mutum 4.
Tashar ta iskar gas na yankin Agbor ne a jihar ta yankin kudu maso kudancin Najeriya.
Gwamnan jihar Ifeanyi Okowa ya nuna kaduwa kan akasin da daukar alwashin kula da jinyar mutanen da su ka samu kunar wuta da ke kwace a gadon asibiti.
Saboda tsananin kunar da mutanen su ka samu, an tura su asibitin koyarwa na jami’ar Benin.
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀