• Sat. May 21st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

MUTUM 9 SUN RASA RAI INDA 50 SU KA SAMU RAUNUKA A HATSARIN MOTA A JIGAWA

ByYusuf Yau

Apr 2, 2022 , ,

Rahotanni daga jihar Jigawa Najeriya na baiyna cewa mutum 9 sun rasa ran su, inda 50 su ka samu raunuka daban-daban a sanadiyyar hatsarin babbar mota a yankin karamar hukumar Ringim.
Babbar motar na dauke da lodin mutane da shanu inda ta ke kan hanyar ta ta tafiya Lagos da ke kudancin Najeriya.
Direban matashi mai suna Babangida Muhammad dan garin Azare a jihar Bauchi ya rasa birkin motar inda hakan ya sa ta samu hatsarin.
An yi wa motar lodi a garin Maigatari da ke jihar ta Jigawa.
Rundunar kiyaye aukuwar hatsari FRSC ta baiyana cewa gudun da ya wuce misali ya haddasa hatsarin.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.