• Mon. Jan 17th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

MUTUM 82 SUN MUTU A GOBARAR ASIBITIN KORONA A IRAKI

ByNoblen

Apr 26, 2021 , ,

An samu gobara a asibitin kula masu fama da cutar korona bairos a Iraki inda mutum 82 su ka rasa ran su.

Wannan abun juyayi ya sa mutane na zargin cin hanci da rashawa da almubazzaranci su ka haddasa akasin.

‘Yan Iraki da su ke cikin wadanda su ka taimaka wajen dauke wadanda su ka samu raunuka, sun bukaci a kori ministan lafiya na kasar Hassan Al-Tamimi wanda duk da ma an dakatar da shi daga aiki.

Gobara ta tashi a asibitin Khatib a birnin Bagadaza inda a ka dora alhakin kan tukwanen iskar shaka da ke da illa.

Ma’aikatar lafiya ta Iraki ta tabbatar da mutuwar mutum 82 da jin raunin mutum  110.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *