• Sun. Dec 5th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

MUTUM 42 SU KA MUTU A SANADIYYAR GOBARA A CIBIYAR MASU KORONA A KUDANCIN IRAKI

ByNoblen

Jul 14, 2021 , ,

Gobara ta yi sanadiyyar mutuwar kimanin mutum 42 a cibiyar killace wadanda annobar korona ta shafa a kudancin Iraki.

Baya ga mutanen da su ka mutu, kazalika sama da mutum 60 sun samu raunuka.
An samu gobarar a asibitin Imam Hussieni a gundumar Djil Qar.

Jami’in lafiya na Iraki Haydar Al-Zamili ya ce kuna ce ta yi sanadiyyar mutuwar mutanen kuma a na cigaba da bincike don fargabar ko akwai wadanda ke makale a cikin ginin.

Tuni firaministan Iraki Mustafa Al-Khadimi ya kara wani taron gaggawa da wasy daga ‘yan majalisar sa don bincika dalilin aukuwar gobarar.
An bukaci hatta likitoci da ke hutu a yankin Dhil Qar su taimaka wajen yi wa wadanda su ka samu raunuka magani.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *