• Sun. Nov 28th, 2021

Noblen tv

Gaskiya Jari…

MUTUM 4 SUN SAMU RAUNI A HARIN DA HOUTHI TA KAI KAN FILIN JIRGIN ABHA

ByHassan Goma

Oct 7, 2021 , ,

 

Mutum 4 ne su ka samu raunuka sanadiyyar harin da ‘yan tawayen houthi na Yaman da Iran ke marawa baya su ka kai cikin Saudiyya.

Harin dai da jirgi marar matuki ya shafi filin saukar jiragen sama ne na Abha da ke kudancin kasar.

Wadanda su ka samu raunukan duk ma’aikatan filin jirgin ne da ya saba ganin irin wadannan hare-hare.

Rundunar samaniya ta gamaiyar larabawa mai taimakawa gwamnatin Yaman, ta lalata bigiren da a ka harbor jirgin da ke lardin Saada na arewa maso yammacin Yaman.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *