• Sun. Jan 16th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

MUTUM 2 SUN RASA RAN SU A SANADIYYAR KORONA BAIROS A SAUDIYYA

Hukumomi a Saudiyya sun baiyana cewa a alhamis din nan mutum 2 sun rasa ran su sanadiyyar kamuwa da korona bairos inda mutum 5,499 su ka kamu da cutar.
A adadin sabbin kamuwa da cutar mutum 1,565 a Riyadh ne, 877 a Jeddah, 474 a Makkah, 239 a Madinah, 198 a Dammam, 137 a Taif, 110 a Qatif, 103 a Alkhobar, 102 a Hofuf, 100 a Khulais inda sauran garuruwa a ka samu kasa da mutum 100 da su ka kamu.
Hakanan adadin wadanda su ka warke ya kai 555,035 bayan karin mutum 2,978 sun samu waraka.
Zuwa yanzu mutum 8,901 sun riga mu gidan gaskiya a kasar ta Saudiyya.
An yi amfani da fiye da alluran rigakafi miliyan 53.3 a Daular.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
2 thoughts on “MUTUM 2 SUN RASA RAN SU A SANADIYYAR KORONA BAIROS A SAUDIYYA”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *