• Thu. Aug 18th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

MUTUM 19 SUN RIGA MU GIDAN GASKIYA A SANADIYYAR HATSARIN MOTA KAN HANYAR KANO ZUWA ZARIA

An samu mummunan hatsarin mota a kan hanyar Kano zuwa Zaria inda mutum 19 su ka rasa ran su, yayin da mutum 26 su ka samu raunuka.
Hatsarin ya auku ne a sanadiyyar taho mu gama na motocin safa biyu da ke gudun da ya wuce kima.
Motocin wadanda na fasinja ne na gudun gaske inda hakan ya sa direbobin su ka kasa shawo kan motocin har a ka samu taho mu gama inda motocin su ka kama da wuta.
Wasu daga wadanda su ka rasa ran su, sun kone duk da haka ‘yan uwan wadan su da su ka rasa ran na su sun gane gawawwakin su, su ka tafi da su.
An kai wadanda su ka samu raunukan asibitin garin Kura a jihar Kano don samun kulawa.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “MUTUM 19 SUN RIGA MU GIDAN GASKIYA A SANADIYYAR HATSARIN MOTA KAN HANYAR KANO ZUWA ZARIA”

Leave a Reply

Your email address will not be published.