• Sat. May 21st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

MUTUM 16 SU KA SAMU RAUNUKA A HARIN HOUTHI KAN JIRGIN SAMAN ABHA NA SAUDIYYA

ByNoblen

Feb 11, 2022 ,

Harin jirgi marar matuki da kungiyar ‘yan tawayen houthi na Yaman su ka kai kan filin jirgin saman Abha na Saudiyya ya haddasa samun raunuka ga mutum 16.
Kakakin rundunar yaki da ‘yan tawayen Burgediya Janar Turki Almaliki ya ce rundunar sama ta Saudiyya ta kange jirgin daga harin inda ta lalata shi amma sassan jikin sa sun fado kan filin jirgin saman da hakan ya raunata mutane.
Almaliki ya ce hari kan filin jirgi da ya shafi farar hula laifin yaki ne da kungiyar ‘yan tawayen ta ‘yan shi’a da Iran ke marawa baya ke aikatawa.
Wannan bas hi ne karo na farko da ‘yan houthi kan cilla makamai cikin Saudiyya ba, kuma an tabbatar makaman kirar Iran ne.
Zuwa yanzu a na cigaba da fafatawa tsakanin ‘yan houthi da dakarun gwamnatin Yaman a fagen daga na arewacin kasar.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
15 thoughts on “MUTUM 16 SU KA SAMU RAUNUKA A HARIN HOUTHI KAN JIRGIN SAMAN ABHA NA SAUDIYYA”

Leave a Reply

Your email address will not be published.