• Mon. May 23rd, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

MUTANE SUN DAKA SAYYADA A ABUJA A SANADIYYAR BABBAN TARON APC

Mutane sun daka sayyada a tsakiyar Abuja sanadiyyar babban taron APC na zaben sabbin shugabanni a dandalin EAGLE da ke tsakiyar birnin.
Datse hanyoyin tsakiyar birnin don samar da tsaro ya sanya ya zama motoci musamman na fasinja da ma wadanda ba manyan ‘yan siyasa ba, ba za su iya yawo ko in aba.
Kasancewar tsananin zafin rana ya sa mutane shiga neman ruwa ido rufe da hakan ya kawo gagarumin ciniki ga masu sayar da ruwa da kunun zaki ko farau-farau.
Hatta jami’an tsaro sun yi likis kuma bas a tsanantawa jama’ar da ke zirga-zirga da kafa don yawan ‘yan siyasar da kuma kasancewar siyasa ta jama’a ce.
Masu son takarar mukamai daban-daban sun manna hotunan su ko an manna a madadin su a ciki da gewayen da’irar taron.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀
One thought on “MUTANE SUN DAKA SAYYADA A ABUJA A SANADIYYAR BABBAN TARON APC”

Leave a Reply

Your email address will not be published.