• Sun. Jan 16th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

MUTANE NA CIGABA DA ZUBAR D HAWAYEN JUYAYI BISA RASUWAR BABBAN SHEHUN MALAMI DR.BAMBA

Jama’a na cigaba da zubar da hawaye na juyayi bisa rasuwar babban shehun malami na hadisi Dr.Ahmad Muhammad Bamba a ranar jumma’a.
A kafar sadarwar yanar gizo a na cigaba da saka wasu daga karatun da malamin ya gabatar tsawon shekaru gommai da kan wayar da kan al’umma kan lamuran addini da rayuwa.
Hakanan karatun na kara kwarin guiwa ga jama’a su rika dogaro ga Allah don samun mafita a duk lokacin jarrabawa da kaucewa matukar bukatar tara abun duniya.
Wani babban abun juyayin shi ne cike gurbin babban malamin d malamai irin su Dr.Mansur Sokoto ke ganin abu ne mai wuya.
An wayi gari kujerar da shehun malamain ke zama don nazari ta na nan ba kowa a kan ta

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *