• Sat. May 21st, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

MUTANE NA CIGABA DA SHARHI KAN BABBAN ZABEN AMURKA

Mutane a Najeriya na cigaba da yin sharhi kan babban zaben Amurka da bambancin sa da na Najeriya musamman bangaren jihohin Amurka masu yawan wakilai da a ke yi wa taken na raba-gardama.

Sharhin ya kara rincabewa bayan shugaban Amurka Donald Trump ya wallafa wani faifan bidiyo da ke nuna wasu mutane a Najeriya sun yi gangami na mara ma sa baya.

Trump ya baiyana gangamin da wata babbar karramawa.
Mutanen dai da su ka gudanar da gangamin ‘yan yankin kudu maso gabashin kasar ne mai akasarin kabilar Igbo.

Hakika duk wanda ya samu nasarar lashe zabe a Amurka ya na da tasiri mai kyau ko akasin hakan ga al’ummar Najeriya da ma nahiyar Afurka.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.