• Thu. Aug 18th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

MUTAN ZAMFARA DA KEBBI NA KOKAWA GA HARE-HAREN BARAYIN DAJI

ByNoblen

Jun 27, 2022 ,

Al’ummar jihar Zamfara da Kebbi na nuna damuwa kan yanda barayin daji su ka sake baiyana da karfin su inda su kan kai hare-hare da sace mutane.

Barayin na shiga kauyuka su sace dukiya da mutane inda hakan yak e barazana ga manoma don ga damuna ta fara karfi amma daji na gagara shiguwa.

Yanzu haka wasu mazauna kauyukan da ‘yan bindiga su ka tayar a jihar Kebbi na zaune a wajen da ya zama sansanin gudun hijira.

Mutanen na bukatar tallafin gwamnati don samun abinci da kuma ingancin tsaro matukar za su koma garuruwan sun a asali.

Jihar Zamfara ta dade cikin wannan fama inda lamarin yanzu kuma ke neman ta’azzara a jihar Kebbi da ke makwabtaka.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published.