• Mon. Jan 17th, 2022

Noblen tv

Gaskiya Jari…

MUSULMI SUN SHIGA JUYAYIN RASUWAR SHEIKH DR.AHMAD IBARHIM BAMBA BUK

Musulmi a Najeriya da wasu kasashen ketare da dama sun shiga juyayin rasuwar babban malamin HADISI Sheikh Dr.Ahmad Ibrahim Bamba BUK.
Marigayin mazaunin Kano ya rasu ne bayan fama da gajeruwar jinya, kuma an gdanar da sallar jana’aizar sa a masallacin Darul Hadith a Kano bayan idar da sallar jumma’a.
Masu juyayi sun yi dafifi don shaida jana’izar da gudanar da addu’ar neman rahama ga marigayin.
Sheikh Dr.Ahmad Bamba ya share kusan shekaru 40 ya na koyar da jama’a ilimin hadisi, tauhidi da sauran fannonin ilimi.
Marigayin ya shahara wajen nuna dattijantaka ga fatawoyin da ya ke bayarwa don fahimtar da jama’a dokokin Allah cikin hikima.

Share this...
Share on Facebook
Facebook
Email this to someone
email
KU KASANCE DA NOBLEN DON SAMUN INGANTATTUN LABARAI A KOWANE LOKACI😀😀😀

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *